Gobara ta Hallaka Mutane da dama a London

Gobara ta Hallaka Mutane da dama a London

Mutane da dama sun hallaka bayan wata mummunar gobara ta tashi cikin dare a wani dogon gini mai hawa 27 a birnin London na Birtaniya.

Mutane da dama sun hallaka bayan wata mummunar gobara ta tashi cikin dare a wani dogon gini mai hawa 27 a birnin London na Birtaniya.

Rahotanni sun ce, akalla jami'an kwana-kwana 200 ne ke aikin kashe wutar gobarar, in da suke amfani da tsanin inji don ceto mutanen da suka makale a ginin na Grenfell Tower.

Kwamishinan ‘yan kwana-kwana na birnin London, Dany Cotton ya ce, akwai mutane da dama da suka mutu a gobarar amma ba zai iya fadin adadinsu ba saboda girman ginin da kuma sassan da ke cikinsa.

Jami’in ya shaida wa manema labarai cewa, wannan ne ibtila’i mafi girma da ya taba gani tun bayan kama aikin kwana-kwana shekaru 29 da suka gabata.

Jami’an kiwon lafiya sun ce, a halin yanzu, akwai fiye da mutane 50 da ke samun kulawa a asibiti.

Ana fargabar cewa, ginin na Grenfell Tower zai ruguje saboda yadda wuta ta yi ma sa mummunan lahani.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani game da musabbabin tashin gobarar wadda ta fara tun da misalin karfe daya na daren da ya gabata.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni