Firai ministar Birtaniya ta tabbatarwa ‘yan kasashen Turai dake da zama a kasar cewa, rayuwarsu ba zata samu canji ba

   Firai ministar Birtaniya ta tabbatarwa ‘yan kasashen Turai dake da zama a kasar cewa, rayuwarsu ba zata samu canji ba

Firai minister Birtaniya Theresa May, tayi kokarin ba miliyoyin ‘yan kasashen Turai dake zama a kasar tabbacin cewa, rayuwarsu da ta iyalansu ba zata sake ba, bayanda Ingila ta fice daga kungiyar Tarayyar Turai a shekara ta dubu biyu da goma sha tara

May tayi tayin ba ‘yan asalin kasashen Kungiyar Tarayyar Turai ‘yancin zama a Birtaniya kamar kowanne bature da aka haifa a Ingila, da wadanda aka haifa Scotland da kuma Wells, da kuma damar kula da lafiyarsu da ilimi, da tallafin marasa galihu, da kuma kudin fensho. Za a yi amfani da dokokin kasar Birtaniya a kan al’umman kasashen Kungiyar Tarayyar Turai ba tare da la’akari da dokokin kotunan kasashen Turai ba.

A wani sako da ta gabatar, May ta fadawa kimanin ‘yan kasashen turai miliyan uku da dubu dari dake zaune a Birtaniya cewa, Muna so ku zauna. Tace burinta shine ta ba dukan wadanda suke zaune a Birtaniya a halin yanzu tabbacin cewa, ba za a ce su fice daga kasar ba lokacin da Birtaniya zata fice daga KTT.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni