Faransa: Tarayyar Turai Zata Mutunta Yarjejeniyar Nukiliya Ta Iran

Faransa: Tarayyar Turai Zata Mutunta Yarjejeniyar Nukiliya Ta Iran

Shugaba Macron na Faransa ne ya bayyana haka a yayin da yake ganawa da jakadun kasar a birnin Paris a jiya Litinin

Emmanuel Macron ya kuma yi suka akan matsayar Amurka dangane da batutuwa daban-daban da su ka hada da ficewarta daga cikin yarjejeniyar Nukiliya sannan ya jaddada cewa; Faransa za ta kare yarjejeniyar Nukiliya

Donald Trump shugaban kasar Amurka ya sanar da ficewar kasarsa daga yarjejeniyar ta Nukiliya ne a ranar 8 ga watan Mayu. Kasashe da dama sun yi tir da matakin na shugaban kasar Amurka, tare da yin kira da a kare yarjejeniyar

Kasashen Faransa, Birtaniya, SIn, Rasha, Jamus da kuma tarayyar turai suna daga cikin masu kokarin ganin yarjejeniyar ba ta rushe ba.

Tarayyar Turai ta yi alkawalin bayar da dukkanin taimakon da za ta iya domin kare yarjejeniyar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky