Erdogan ya gargadi masu sa ido kan zaben Turkiya

Erdogan ya gargadi masu sa ido kan zaben Turkiya

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gargadi masu sa ido daga kasashen duniya da wuce gona da iri bayan sun bayyana shakku game da sahihancin zaben raba gardama da al’ummar kasar suka gudanar don fadada karfin ikonsa.

A wani jawabi da ya yi wa dandazon magoya bayansa a farfajiyar fadar gwamnatinsa, shugaba Erdogan ya fada wa masu sanya idon da su tsaya in da Allah ya ajiye su.

Wannan na zuwa ne bayan wasu kungiyoyi na ‘yan kallo masu zaman kansu da suka hada da OSCE da ODIHR da PACE da ke nahiyar Turai, sun fitar da rahotansu kan zaben raba gardamar da ‘yan adawa suka lashi takobin kalunbalantar sakamakonsa.

A kokarin kare matakin da ya dauka, shugaba Erdogan ya ce, Turkiyya ta gudanar da zabe na Demokradiya da babu wata kasa a yankin yammacin duniya da taba gudanar da irinsa .

Shugaban ya kuma ce, akwai yiwuwar ya sake shirya wani zaben raga gardamar kan yunkurinsu na neman kujera a kungiyar kasashen Turai da kuma sake dawo da hukuncin kisa a kasar.

A yayin da wasu kasashen duniya ke nuna rashin gamsuwa kan sakamakon zaben, ita kuwa Saudiya da ta kasance aminiyar Turkiyya, ta yaba da nasarar da Erdogan ya samu da za ta kara ma sa karfin iko kan karagar mulki.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds hanyar Shahidai
Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky