'Dan Bindiga Ya Kashe Mutane Biyu A Gidan Rawa Na Kasar Jamus

  'Dan Bindiga Ya Kashe Mutane Biyu A Gidan Rawa Na Kasar Jamus

A kasar Jamus mutane biyu sun gamu da ajalinsu a wani gidan rawa, wasu mutanen hudu kuma suka jikkata sakamakon hare-harbe a wani gidan rawa kafin wayewar gari yau lahadi.

Wata sanarwa daga ‘yan sandan kasar na cewa wani mutun mai kimanin shekaru 34 ya aikata harbe-harben.

Sanarwar ‘yan sandan na cewa an jikkata maharin a lokacin da ‘yan sanda ke kokarin kama shi yana shirin tserewa don barin  gidan rawan amma kuma daga bisani ya mutu a asibiti.

Wannan hari na zuwa ne kwanaki biyu bayan wani harin da wani mutun dauke da wuka ya kai shagon saida kayayyaki inda aka sami hasarar rayuka a garin Hamburg


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni