Burtaniya: Jam'iyyar Conservertive Ba Ta Samu Rinjayen Da Take Bukata Ba

Burtaniya: Jam'iyyar Conservertive Ba Ta Samu Rinjayen Da Take Bukata Ba

Rahotanni daga Burtaniya na nuni da cewa sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin da aka gudanar jiya, jam'iyyar Conservative mai mulki ba ta samu rinjayen da take bukata ba.

Jam'iyyar ta Conservative dai wadda ya ta samu kujeru 326 daga cikin kujeru 650 na majalisar ya zuwa yanzu da ake gab da kammala kidaya kuri'un baki daya, hakan na nuni da cewa ba za ta iya kafa gwamnati ita kadai ba.

An dai gudanar da zaben ne na ba zata bayan da Fira ministar Burtaniya Theresa May ta bukaci hakan a cikin watan Afirilun da ya gabata, bisa zaton cewa za ta samu gagarumin rinjayen da zai bata damar kafa gwamnati ita kadai.

Yanzu dai ana sa ran jam'iyyar ta Conservative za ta yi hadaka da wata jam'iyyar ne ne domin kafa gwamnati, yayin da shi kuma shugaban jam'iyyar Labour Jeremy Corbyn wanda jam'iyyarsa take a matsai na biyu, ya bayyana hakan a matsayin babban ci gaba ta fuskar dimukradiyya.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni