Boris Johnson Martani Yaci Mutunci Hijabi

Boris Johnson Martani Yaci Mutunci Hijabi

Shugaban Jam'iyyar Conservative na kasar Birtaniya Brandon Lewis ya kirayi tsohon ministan harkokin Wajen Birtaniyan Boris Johnson da ya nemi gafara akan cin zarafin da ya yi wa mata musulmi masu sanya nikabi

Boris Johnson ya kwantanta  matan masu sanya kallabin da su ke rufe fuskarsu da shi, Burkaa da cewa;  sun yi kama da masu fashi da makami a cikin Banki.

Shi ma Alistair Burt da shi ne babban jami'i mai kula da harkokin Afirka da gabas ta tsakiya a ma'aikatar harkokin wajen Birtaniy, ya ce furucin na Johnson cin zarafi ne.

Ita ma Majalisar musulmin Birtaniya ta bukaci ganin tsohon ministan harkokin wajen na Birtaniya ya nemi gafara.

A cikin watannin bayan nan a nahiyar turai an tsananta muzanta suturar hijabi da matan musulmi suke sanyawa.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky