Anyi zanga zangar Allah wadai da HK Isra'ila a Faransa

Anyi zanga zangar Allah wadai da HK Isra'ila a Faransa

Jama'a sun gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da bakar siyasar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kan al'ummar Palasdinu a dandalin Chetelet da ke birnin Paris na kasar Faransa.

Masu zanga-zangar da suka fito daga kungiyoyin kare hakkin bil-Adama da dama gami da baki 'yan kasashen waje da kuma 'yan kasar ta Faransa sun gudanar da taron gangami ne a dandalin Chetelet da ke birnin Paris na kasar ta Faransa suna rera taken yin Allah wadai da bakar siyasar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kan al'ummar Palasdinu tare da jaddada bukatar kauracewa duk wasu kayayyaki da suka fito daga haramtacciyar kasar ta Isra'ila.

Masu zanga-zangar sun fito ne domin jaddada rashin amincewarsu da bakar siyasar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta ci gaba da mamaye yankunan Palasdinawa musamman a gabar yammacin kogin Jordan da nufin gudanar da gine-ginen matsugunan yahudawan sahayoniyya 'yan kaka gida.

Jami'an 'yan sandan Faransa dai sun kai dauki zuwa dandalin domin bada kariya ga masu zanga-zangar ta lumana domin bayyana ra'ayinsu kan bakar siyasar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds hanyar Shahidai
Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky