An Kara Tsayin Dokar Ta Baci A Turkiyya

 An Kara Tsayin Dokar Ta Baci A Turkiyya

Shugaban Turkiya Racep Tayyib Erdogan ya fadada dokar ta baci a hukumance da aka kafa bayan wani juyin mulki a shekarar 2016 da bai yi nasara ba, yana cewar za a ci gaba da wannan dokar har sai kasar ta samu cikakken kwanciyar hankali da zaman lafiya.

Erdogan ya bayyana haka ne a jiya Lahadi a birnin Ankara gaban dubban mabiyansa da yan jami’iyarsu ta Justice and Development Party da suka kira da a sake zaben dayan uban jami’iyasu ya ci gaba da rike mukamin.

Wannan dokar ta bacin, ta na baiwa Erdogan da hukumar zantarwarsa damar kafa dokoki ba tare da umarnin majalisa ba ko shawarar sashen shari’a.

Sanarwa Erdogan da kuma sake dawowa ya nemi mukamin shugaban jami’iya ya zo ne bayan mako hudu da Turkiya ta gudanar da wata kuri’ar raba gardama a kan fadada ikon shugaban wanda ya yi karamin nasara a kuri’ar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni