An Kara Kama Wasu Mutane Biyu Sakamakon Harin Da Aka Kai A London

An Kara Kama Wasu Mutane Biyu Sakamakon Harin Da Aka Kai A London

Jiya Juma’a Jami’an ‘Yan Sanda a London sunce sun kama karin wasu mutane guda biyu dangane da harin da aka kai a kusa da Majalisa.

Kwamandan Jami’an ‘Yansandan Hana Afkuwar Aiyukan ta’addanci Mark Rowley ya bayyana kamen a matsayin mai muhimmanci, koda yake bai bada wani cikakken bayani ba . Yace mutane 9 na nan a tsare kuma an saki wani mutum guda.

Jami’an ‘Yan sanda sun bayyana wanda yakai harin ya kuma kashe mutane hudu a kusa da Majalisa da sunan Khalid Masood, dan kasar Birtaniya wanda ya shiga cikin addinin Islama kuma yana da tsohon tarihin aikata manyan laifuffuka na mallakar makamai da sauransu.

Rowley yace sunan Masood na yanka shine Adrian Russell Ajao. Kungiyar Da’esh tace Masood, dan shekara 52 Sojanta ne wanda ya amsa kiran kai hari kan fararen hula da kuma jami’an soji a kasashen da suke kawance da Amurka masu yakar Kungiyar ta Da’esh.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds hanyar Shahidai
Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky