Shugabannin Iran Da Turkiyya Sun Bayyana Rashin Amincewa Da Rarraba Kasar Iraki

Shugabannin Iran Da Turkiyya Sun Bayyana Rashin Amincewa Da Rarraba Kasar Iraki

Shugabannin kasashen Iran da Turkiyya sun bayyana cewa ba za su taba amincewa da kokarin Kurdawa na rarraba kasar Iraki ba, suna masu sake jaddada shirin gwamnatocinsu na kara karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Hasan Ruhani na Iran da Rajab Tayyip Erdogan na Turkiyya sun bayyana hakan ne a wata ganawa da manema labarai da suka yi a yau din nan jim kadan bayan tattaunawar da suka yi a tsakaninsu a ci gaba da ziyarar da shugaban Turkiyyan yake yi a Iran inda har ila yau suka jaddada wajibcin hadin kai tsakanin kasashen musulmi.

A nasa bangaren shugaba Ruhani ya ce babban burin Iran shi ne ganin an kiyaye hadin kan al'ummar kasar Iraki da rashin rarraba kasar don haka ne za su ci gaba da daukar matakan da suka dace tare da kasashen Iraki da Turkiyyan wajen ganin ba a rarraba kasar Irakin ba yana mai kakkausar suka ga shirin 'yan siyasar yankin Kurdestan na Iraki na ballewa daga kasar Irakin inda ya ce hakan babban kuskure ne.

Shi ma a nasa bangaren shugaban kasar Turkiyyan Rajab Tayyip Erdogan ya bayyana cewa ba za su taba amincewa da zaben raba gardamar balle yankin Kurdestan na Iraki daga kasar ba wanda yace babu wata kasa a duniya da ta amince da hakan in ba haramtacciyar kasar Isra'ila ba.

A yau ne dai shugaban Turkiyya  ya kawo ziyarar aiki nan Tehran don ganawa da manyan jami'an kasar da kuma tattaunawa kan alakar da ke tsakaninsu kasashen biyu da kuma batun da ya shafi yankin Gabas ta tsakiya musamman batun shirin Kurdawa na ballewa daga kasar Iraki.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky