Sakon Imam Khamene'i Zuwa Ga Alhazan Shekarar Bana 1439

Sakon Imam Khamene'i Zuwa Ga Alhazan Shekarar Bana 1439

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai, Godiya Ta tabbata ga Allah, tsira da aminci su tabbata ga manzonsa al-Mustafa da iyalansa tsarkaka da sahabbansa zababbu

Allah madaukakin sarki yana fadin cewa; Kuma  Ka yi shela cikin mutane saboda yin haji, za su zo maka matafiya a kasa da kuma kan kowane rakumi, za su zo maka daga kowane lungu mai nisa.

Wannan kiran na Allah bai gushe yana kiran mutane ba a tsawon karnuka da zamuna akan su taru a cibiyar tauhidi.  Wannan kiran da annabi Ibrahim ya yi yana nufin dukkanin mutane ne, wanda kuma yake abin alfahari a gare su; Duk da cewa wani sashe na mutane bai ji wannan kiran da kunnuwansu ba kuma wasu zukatan za su ci gaba da zama  haramci saboda kasantuwar su cikin shamaki na rafkanuwa da jahilci, kuma duk da cewa wani sashe na mutane ba su yin tanadin na ruhi da zai sa su iya yin tarayya a cikin wannan bakunta ta duniya ba wacce kuma take dawwamammiya, ko kuma saoboda wasu dalilai ba za su sami damar zuwa ba.

A halin yanzu ku-mahajjata-kuna cikin wannan baiwa, kuna cikin bagire na amincin wanda Allah ne mai karbar bakunci.  Wuraren irin su filin Arafah, Mash'ar, da Mina da safa da marwa da dakin Allah, da masallacin harami da masallacin annabi, da dukkanin wuraren da suke da alaka da aikin hajji, kowane daya daga cikinsu wani sashe ne na tsararrun ayyukan tsarkake ruhi ga alhazai da suke da masaniya akan darajar wannan dace da su ka samu, suke kuma cin moriyarsa domin tsarkake kawukansu da mayar da shi zama guzuri na rayuwa.

Batu mai muhimmanci wanda yake jan hankali kowane ma'abocin tunani, shi ne ayyana wani wuri guda na taurwar mutane daga konwane shekaru, kuma a wani lokaci guda. Kadaicin lokaci da kuma wuri suna daga cikin babban sirrin aikin hajji.

Shakka babu wannan taron na shekara-shekara da al'ummar musulmi suke yi a daura da dakin Allah shi ne yake fassara ma'anar "Don su halarci amfanin da za su samu".  Wannan ita ce babbar alamar hadin kai a tsakanin al'ummar musulmi, kuma abin da yake nuni zuwa gina al'ummar musulmi wanda ya zama wajibi ya kasance a karkashin inuwar dakin Allah. Daki ne wanda na kowane, mazaunin cikinsa da mai zuwa daga waje."

Yin aikin Hajji a acikin wannan bagire kuma a cikin lokaci guda, kira ne , a cikin hafshe mai sauki wanda kowa zai fahimta ga musulmi da su zama masu hadin kai a koyaushe kuma a cikin dukkanin shekaru.

Akasin haka shi ne abin da makiyan musulunci da musulmi suke so, wadannan da a kowane zamani da lokaci suke ingiza musulmi su zama masu fada da junansu.

 Ku yi la'akari da mummunar halayyar Amurka ma'abociyar girman kai mai tafka laifuka. Kunna wutar yaki a cikin musulunci da musulmi shi ne ginshikin siyasarta. Abin da take so wanda kuma take gogoriyo akansa shi ne haddasa fadace-fadace a tsakanin musulmi, da kuma sakin hannun azzalumai su ci gaba da zalunci raunana. Haka nan  goyon bayan azzalumi da kuma murkushe mai rauni ta hanyar amfani da karfi fiye da kima da kuma kyale wutar fitinar da ta kunna ta ci gaba da tashi tana hankoro.

Wajibi ne ga musulmi da su kasance cikin fadaka, su kuma rusa wannan siyasar ta shaidanci. Aikin haji kuwa shi ne wurin da za a yi wannan fadakarwar. Wannan kuma shi ne falsafar shelar kubuta daga mushrikai da masu girman kai a yayin aikin haji.

Ambaton Allah shi ne ruhin aikin hajji. Don haka mu raya zukatanmu da wannan ruwan na rahamar Allah, mu kuma sa nishadi a cikin rayuwar,  kuma dogaro da jingina da shi su ne mabubbugar karfi da daukaka da adalci a kyawu.

A hali irin wannan ne za mu iya samun nasara akan makircin makiya.

Ya ku alhazai masu girma, ka da ku manta da yi wa al'ummar musulmi addu'a haka nan raunana a cikin kasashen Syria, Irak,i pakasdinu, Afghanistan, Yemen, Bahrain, Libya, Pakistan, Kashmir, Burma da sauran yankunan duniya.

Ku roki Allah ya rusa karfin Amurka da sauran masu girman kai, da 'yan korensu.

Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullah Wa Barakatuhu.

Sayyid Ali Khamne'i

28 ga watan Murdada 1397/ 7 ga watan Zul Hijjah 1439
........
300


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds hanyar Shahidai
Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky