Rasha: Iran Tana Yaki Da Ta'addanci A Yankin Gabas Ta Tsakiya

Rasha: Iran Tana Yaki Da Ta'addanci A Yankin Gabas Ta Tsakiya

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergie Lavrov ya bayyana kasar Iran a matsayin kasar da take yaki da ta'addanci a yankin gabas tsakiya.

Sergie Lavrov ya bayyana hakan ne a wata zantawa da ta hada shi da mujallar National Interest ta kasar Amurka, inda ya bayyana cewa Iran tana da babban tasiri a yankin gabas ta tsakiya, kuma tana yaki da ta'addanci a yankin, kuma Rasha tana yin aiki na hadin gwiwa tare da Iran a wannan bangare, domin wanzar da sulhu da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

Dangane da kungiyar Hizbulla da kuma rawar da take takawa kuwa, ministan harkokin wajen kasar ta Rasha ya bayyana cewa; kungiyar Hizbullah tana taka gagarumar rawa  a fagen yaki da 'yan ta'adda, a daiai lokacin da gwamnatin Amurka da wasu daga cikin gwamnatocin larabawa na yankin suke ta hankoron ganin ganin sun taimaka ma 'yan ta'addan.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni