Limamin Juma'ar Tehran: Amurka Ta Gama Karya Yejejeniyar Nukiliya

Limamin Juma'ar Tehran: Amurka Ta Gama Karya Yejejeniyar Nukiliya

Ayatullah Ahmad Khatami wanda yake magana akan matsayar Amurka dangane da yarjejeniyar Nukiliyar, ya ce; Babu wani abu da ya saura da Amurkan ba ta take ba

Limamin na Tehran ya ci gaba da cewa; A lokuta da dama jami'an gwamnatin Iran sun sha bayyana cewa; Babu fagen sake kulla wata sabuwar yarjejeniyar ta Nukiliya, wanda hakan shi ne daidai.

Har ila yau, limamin juma'ar ya yi ishara da yadda kasashen Turai suke goyon bayan ci gaba da aiki da yarjejeniyar, sannan ya kara da cewa; Idan har turawan za su fuskanci zabi tsakanin mu'amala da Iran ko Amurka za su zabi Amurka ne.

A cikin kwanakin bayan nan, Amurka tana yin magana akan yarjejeniyar Nukiliyar Iran tare da kokarin sauya ta, ko yin watsi da ita.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky