Kasar Iran Ta Aika Da Sakon Taya Murna Ga Shuwagabannin Iraki

 Kasar Iran Ta Aika Da Sakon Taya Murna Ga Shuwagabannin Iraki

Shugaban Jamhuriyar musulinci ta Iran Dakta Hasan Rauhani ya mika sakon mura ga Shugaban kasar Iraki, Firaminsta, Ayatollah Sistani na nasarar da kasar ta yi na tsarkake 'yan ta'addar ISIS daga Mosil babban birnin Jihar Nainuwa dake arewacin kasar

Kafar watsa labaran fadar Shugaban Kasar Iran ya habarta cewa a sakon tayar murna da Shugaba Rauhani ya aikewa takwaransa na kasar Iraki a wannan Juma'a dangane da nasarar da kasar ta samu na tsarkake 'yan ta'adda daga Mosil ya bayyana cewa kyakkyawan canjin tsaro da ya samu a Iraki tare da nasarar da aka samu na yaki da 'yan ta'adda sakamakon kokarin Sojoji da Al'ummar kasar ne da kuma taimakon makwabtan kasar wajen kawo karshen kungiyar ta'addancin ISIS da masu goyan bayan su baki baya.

A wasikar da ya aikewa Piraministan kasar Iraki Haidar Abadi, Shugaba Rauhani ya ce wannan Babbar nasara da aka samu na zuwa bisa taimakon aiki tare, sadaukar da kai, kokarin Al'ummar kasar, Dakarun tsaro,Dakarun sa kai na Hashadu Sha'abi da kuma goyon bayan makwabtan kasar, wannan shi ke nuna mahimancin yaki da 'yan ta'adda azzalimai masu kashe Mutane da sunan musulinci.

A sakon da ya aikewa babban Malamin Addinin nan Ayatollah Sistany, Dakta hasan Rauhani ya ce Nasarar da Al'ummar kasar Iraki ta samu wajen 'yanto garin Mosil daga 'yan ta'addar ISIS ya kara bayyanawa Duniya mahimancin fataha da kuma matsayin Marja'iya a musulinci.

Shugaba Rauhani ya ce Shekaru uku da suka gabata Al'ummar Iraki sun shiga wani yanayi na damuwa da takaici bayan da 'yan ta'addar ISIS suka mamaye wani bangare na kasar, cibiyar marja'iyar ce ta medowa Al'ummar kasar fata da kuma basu karfin gwiwa wajen tunkarar 'yan ta'addar da kuma yakar su, da hakan yayi sanadiyar tashin Al'umma da Dakarun kasar wajen kalubalantar 'yan ta'addar masu fice gona da iri.

A yau Juma'a ce Tashar Telbijin din kasar ta Iraki ta bayar da labarin kawo karshen kungiyar Da'esh a Mosil.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky