Jagora: Lallai Yakamata A Isar Da Sakon Siyasar Juyin Juya Halin Musulunci A Iran Ga Musulmi A Hajja

Jagora: Lallai Yakamata A Isar Da Sakon Siyasar Juyin Juya Halin Musulunci A Iran Ga Musulmi A Hajja

Jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Aya. Sayyid Aliyul Khaminae ya jaddada bukatar a isarda sakon siyasa na juyin juya halin musulunci a nan Iran ga al-ummar musulmi a ayyukan hajji.

Aya. Sayyid Aliyul Khaminai ya bayyana haka ne a yau litinin a lokacinda yake ganawa da jami'an hukumar Hajji a gidansa a nan birnin Tehran. 

Jagoran ya kara da cewa haduwa da daddaikun musulmi daga kasashen duniya daban daban, sannan a kawar da rashin fahintar da sukewa musulman Iran da ma addinin musulunci yana daga cikin abubuwan da suke karfafa dangantaka Iran da sauran musulmi a duniya.

Dangane da kokarin da hukumomin kasar Saudia suke yi na hana karatun "Du'a'ul Kumai a lokacin hajji kuma, ya ce dole ne a yi kokarin kauda duk shingen da zai hana hakan.

Aya. Khamana'i ya yi suka kan yadda sarakunan kasar saudia suke rurruka wurare na tarihi wadanda suke nuna rayuwar manzon Allah (s) da sahabbai da kuma mujahidan a farko musulunci da sunan fadada wuraren ayyukan hajji. Jagoran ya kara da cewa a dai-dai lokacinda wasu kasashe suke kokarin kare abubuwan tarihi na kasashensu har ma sukan gina wasu ma da kansu don raya al-adun kasashen sai gashi a Makka da Madina aka shafe abubuwan tarihi na musulunci da ke cikinsu.

Daga karshe ya kammala da cewa wajibin hukumar Hajja da Umara da kuma sauran wadanda abin ya shafa su taimakawa sauran kasashen musulmi kan adana tarihin musulunci da ke kasashensu.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky