Iran : Zamu Ci Gaba Da Karfafa Aikin Sojinmu_Rohani

Iran : Zamu Ci Gaba Da Karfafa Aikin Sojinmu_Rohani

Shugaban Jamhuriya Musulinci ta Iran Hassan Rohani ya jaddada cewa kasarsa za ta ci gaba da karkafa aikin sojinta a dukkan fannoni ciki har da na makamai masu linzami.

Dr Rohani na bayyana hakan ne a yayin faretin sojojin kasar a nan Tehran, wanda ake kira da ''makon kare kai'' wanda ake gudanarwa a zagayowar ranar kaddamar da yakin Iran-Irak a shekara 1980. 

Babban manufar wannan a cewar shugaba Rohani, shi ne daidaita sahu da sauren kasashen yankin irinsu Isra'ila da Saudiyya wadanda ke kashe bilyoyin daloli don sayen makamai daga kasashen yamma musamen Amurka.

Sannan ya kara da cewa Iran zata karfafa aikin sojinta a kasa da sama dana ruwa,  da kara karfinta a yankin, wannan kuma ba tare da neman izinin wata kasa a duniya ba.

A yayin faretin, dakarun Iran sun gabatar da wani sabon makami mai linzami da akayi wa lakabi da ''Khoramshahr'' mai cin matsakaicin zango wanda ke iya kai wa nisan kilomita 2,000 kuma makamin zai iya daukar makamai masu yawa,  

Hukumomin Iran sun sanar da cewa suna da karfin fusaha da zasu iya kara karfin makaman su masu linzami wanda aka takaita a yanzu zuwa kilomita 2,000 sai dai kuma acewarsa ba'ayi su ba don goya masu makaman nukiliya ba.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky