Iran Ta Yi Watsi Da Damuwar Da NATO Ta Nuna Kan Shirinta Na Makamai Masu Linzami

Iran Ta Yi Watsi Da Damuwar Da NATO Ta Nuna Kan Shirinta Na Makamai Masu Linzami

Gwamnatin kasar Iran ta yi watsi da damuwar da shuwagabannin kasashe a kungiyar tsaro ta NATO suka nuna dangane da shirin tsaron kasar a taronsu na ranar Laraban da ta gabata a birnin Brussels na kasar Belgium

Tashar talabijan ta Presstv a nan tehran ta nakalto kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasimi yana fadar haka a jiya Alhamis. Ya kuma kara da cewa Iran ta yi allawadai da rahoton bayan taro wanda kungiyar ta fitar bayan taron shuwagabannin kasashenta a ranar Laraban da ta gabata, wanda ya nuna cewa shirin makamai masu linzamin kasar da kuma rawan da take takawa a gabas ta tsakiya abin damuwa ne a garesu.

Qasimi ya kara da cewa gwamnatin kasar Iran tana bin duddugin taron na NATO a ranar Laraba, kuma ta gano cewa shugaban kasar Iran ne ya takura sauran kasashen wajen daukar wannan matakin.

Kasar Amurka ce dai take bada mafi yawan kudaden da kungiyar NATO take kashewa, don haka ne kuma take amfani da damar wajen tilasta masu ra'ayinta.

Qasima ya kara da cewa kasar Iran ba zata taba dakatar da shiringta na makamai masu linzami ba don da shi take kare diyaucin mutanen kasarta, sannan dangane da shirin na makamashin nucliya kuma hukumar IAEA ta wadarta wajen tabbatar da wufintar shirin daga ayyukan soje.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky