Iran Ta Yi Tofin Allah Tsine Kan Yunkurin Kai Harin Ta'addanci Kan Haramin Makkah

Iran Ta Yi Tofin Allah Tsine Kan Yunkurin Kai Harin Ta'addanci Kan Haramin Makkah

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi tofin Allah tsine kan yunkurin kai harin ta'addanci kan haramin Makkah tare da jaddada bukatar fadakar al'ummar yankin gabas ta tsakiya kan hatsarin ayyukan ta'addanci.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahroum Qasimi a yau Asabar ya yi tofin Allah tsine kan yunkurin kai harin ta'addanci kan haramin Makkah tare da fayyace cewa: Wannan yunkuri yana nuni da cewa ne akidar ta'addanci wata babbar barazana ce ga duniya musamman ga al'ummar musulmi da kasashensu, kuma yunkurin kai harin ta'addanci kan haramin Makkah lamari ne da ke fayyace cewa: Akidar ta'ddanci bata da alaka da addini, mazhaba , yanki ko al'umma.

Qasimi ya kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana Allah wadai da duk wani aikin ta'addanci a kowane sako na duniya kuma a shirye take ta gabatar da gudumawarta wajen murkushe 'yan ta'adda da ayyukan ta'addanci a duniya.

A jiya Juma'a ce wani dan kunan bakin wake ya tarwatsa kansa a cikin haramin Makkah bayan da jami'an tsaron Saudiyya suka masa kawanya bayan samun bayanan asiri kan mummunar aniyarsa ta kai harin wuce gona da iri kan al'ummar musulmi a karshen Juma'ar watan ramadana mai alfarma.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky