Iran Ta Yabawa Saudiyya Kan Nasara Shirya Aikin Hajjin Bana

Iran Ta Yabawa Saudiyya Kan Nasara Shirya Aikin Hajjin Bana

Jamhuriya musulinci ta Iran ta yi godiya ga kasar Saudiyya kan yadda ta shirya aikin hajjin bana cikin nasara.

Da yake bayyana hakan a gidanb talabijin din kasar, wakilin jagoran juyin juya halin kasar ta Iran, Ali Ghazi-Asghar ya ce munawa Saudiyya godiya kan sabon tsarinta na bana da kuma yadda ta martaba mahajattanmu. 

Duk da rikicin diplomatsiyya dake tsakanin kasashen biyu, sama da mahajjatan Iran 86,000 ne suka sauke farali a kasa mai tsarki a hajji bana, sabanin kauracewa hajji da mahajatan sukayi a shekara 2016 data gabata sakamakon turmutsutsun da aka samu wajen jifar shaidan a hajjin shekara 2015.

Wakilin jagoran juyin juya halin kasar ta Iran, Ali Ghazi-Asghar ya ce yanzu bayan hajiin na bana, wata dama ce ta samu ga kasashen biyu na su tattauna hanyoyin magance sauren sabanin dake tsakaninsu, kamar yadda kamfanin dilancin labaren kasar ta Iran ISNA ya rawaito.

Kasashen Iran da Saudiyya dai na da sabani akan rikece rikicen dake faruwa a kasashen Siriya, Yamen da kuma halin da ake ciki a Bahrain.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky