Iran Na Mutunta Yarjejeniyar Nukiliya - AIEA

Iran Na Mutunta Yarjejeniyar Nukiliya - AIEA

Hukumar kula da makamashi ta kasa da kasa (AIEA) ta ce Iran na ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar data cimma da mayan kasashen duniya.

A sabon rahoton data fitar yau Juma'a kamar yadda ta saba a kowanne watanni uku, hukumar ta kuma ce a tsawan wannan lokaci Iran bata sake tatse urenium ba ko kuma aje sinadarin uremium da ya kai mizanin da ya wuce ka'ida ba.

Hakan dai na nufin Iran bata sabawa yarjejeniyar data cimma da kasashen ba, wanda kuma abin yabawa ne da zai bada damar ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar data fara aiki a watan janairu na shekara 2016 wanda ya kai ga yayewa Iran din takunkumin kasa da kasa da aka kakaba mata musamen kan shirinta na makamashi.

Duk da cewa dai sabuwar gwamnatin Donald Trump ta ce zata ci gaba da aiki da yarjejeniyar da aka cimma a lokacin tsohon shugaba Barack Obama, har yanzu dai akwai babban sabani tsakanin mahukuntan Teheran da na Washington.

A kwanan baya ma dai ma'aikatar kudi ta Amurka ta ce sake kakabawa wasu jami'an Iran takunkumi, lamarin da Iran din ta yi Allah wadai da shi da kakkausar murya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky