Iran: Maganganun Salman Na Nuni Da Cewa Saudiyya Ita Ce Tushen Yada Ta'addanci

Iran: Maganganun Salman Na Nuni Da Cewa Saudiyya Ita Ce Tushen Yada Ta'addanci

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewar maganganun mataimakin yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, wata shaida ce da ke tabbatar da cewa Saudiyya tana ci gaba da gudanar da siyasar lalata yankin Gabas ta tsakiya da yada ayyukan ta'addanci ne.

Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran Bahram Qassemi ne ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani ga kalaman Yarima Mohammed bin Salman din na toshe duk wata kofa ta kyautatuwar alakar tsakanin Iran da Saudiyya.

Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen na Iran ya kara da cewa cikin shekarun da suka gabata Iran ta nuna kyakkyawar aniyar da take da shi cimma yarjejeniyar fahimtar juna tsakaninta da dukkanin kasashen yankin, yana mai cewa dukkanin rikicin da ke faruwa a yankin ya samo asali ne sakamakon tsoma bakin kasashen waje da kuma ayyukan ta'addancin kungiyoyin 'yan takfiriyya da suka samo asali daga akidar wahabiyanci da Saudiyya take yadawa.

A ranar Talatar da ta gabata ce Muhammad bn Salman, wanda kuma shi ne ministan tsaron Saudiyya yayi watsi da duk wani kokari na kawo karshen kai ruwa ranar da ke tsakanin kasashen biyu bayan da Iran ta sanar da yiyuwar kyautatuwar alaka tsakaninta da Saudiyya idan har Saudiyyan ta dakatar da hare-haren wuce gona da irin da take kai wa kan al'ummar kasar Yemen.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky