Iran : Kasar Saudiyya Na Da Hannu A Hare-Haren Ta'addan Da Suka Faru A Makon Baya

 Iran : Kasar  Saudiyya  Na Da  Hannu   A Hare-Haren   Ta'addan  Da Suka Faru A Makon Baya

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ne ya bayyana cewar Iran tana da bayanai na sirri da suke nuni da cewa Saudiyya tana ci gaba da goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'addan da suke kan iyakokin kasar Iran da suke da shirin kai hare-haren ta'addanci cikin kasar.

Zarif ya bayyana hakan ne a jawabin da yayi wajen taron Oslo na kasar Norway a jiya Talata inda ya ce muna da bayanai na sirri da suke nuni da cewa Saudiyya tana ci gaba da goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'adda da suke kan iyakokin Iran na gabas da kuma yammaci, yana mai ishara da maganganun ministan tsaro kana kuma Yariman Yarima mai jiran gado na Saudiyya na cewa za su shigar da yaki cikin gidan Iran.

Ministan ya kara da cewa ko shakka babu jami'an tsaron kasar Iran suna ci gaba da sanya idanuwansu kan iyakokin kasar kuma za su mayar da kakkausan martani ga duk wata barazana ga tsaron cikin kasar Iran.

A watan da ya wuce ne dai ministan tsaro kuma Yariman Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman ya bayyana cewar Saudiyya za ta yi kokarinta wajen tura yaki zuwa cikin kasar Iran. Sannan kuma a ranar 6 ga watan Yunin nan kwana guda kafin harin ta'addancin da 'yan kungiyar ISIS suka kawo Tehran, ministan harkokin wajen Saudiyyan Adel al-Jubeir ya bayyana cewar wajibi ne a "azabtar" da Iran saboda abin da ya kira "tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashen yankin nan" lamarin da da dama suke jingina shi ga harin ta'addancin da aka kawo Iran din bisa la'akari da alakar da ke tsakanin kungiyar ISIS din da kasar Saudiyya.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky