Iran : Jagoran Juyin Islama Ya Gana Da Ma'aikata

Iran : Jagoran Juyin Islama Ya Gana Da Ma'aikata

Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya gana da wani adadi na ma'aikatan kasar a jajibirin ranar ma'aikata ta duniya.

A yayin ganawarsa da ma'aikatan jagoran ya dauko batun babban zaben kasar dake tafe wanda a cewarsa yake da mahimmanci da tasiri akan tsaron kasa.

Jogoran ya ce hadin kan al'umma wani yanayi ne dake tsonewa makiya ido, ma'ana idan suka ga al'umma na da hadin kai to zasu yi dari-dari akan yunkurinsu na neman wargazata musamen kasashe dake bisa turbar Islama kamar Iran.

A gobe daya ga watan Mayu ne ake gudanar da ranar ma'aikata ta duniya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky