Iran: Ba Mu Da Shirin Tattaunawa Da Amurka Kan Wani Batu Na Daban

Iran: Ba Mu Da Shirin Tattaunawa Da Amurka Kan Wani Batu Na Daban

Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qassemi yayi watsi da labaran da wasu kafafen watsa labarai suke watsawa kan tattaunawar da Iran take yi da Amurka inda ya ce Iran ba ta shirin tattaunawa da Amurka kan wani batu na daban in ban da batun tattaunawar nukiliya.

Kamfanin dillancin labaran Iran (IRNA) ya bayyana cewar kakakin Ma'aikatar harkokin wajen ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai a yau din nan Litinin inda ya ce babu gaskiya cikin labarin da ke cewa Iran tana tattaunawa da Amurka kan wani batu na daban. Kakakin ya kara tattaunawar da Iran ta yi da Amurka kan shirin nukiliya ne kuma mai yiyuwa ya ci gaba.

Mr. Qassemi ya ce: Babu wata tattaunawa da ta gudana tsakanin Iran da Amurka, kuma har ya zuwa yanzu, Iran tana nan kan bakanta na kin tattaunawa da Amurka kan wani batu in ba na nukiliyan ba.

Cikin 'yan kwanakin nan dai wasu kafafen watsa labarai sun yada labarin cewa Iran da Amurka sun gudanar da tattaunawa kan wasu batutuwa na daban a bayan fagen taron hadin gwuiwa kan batun nukiliya da ya gudana tsakanin Iran da kasashen duniya da suke cikin tattaunawar nukiliyan.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky