Iran : An Tantance Maharan Da Suka Kashe Mutane 17 A Tehran

Iran : An Tantance Maharan Da Suka Kashe Mutane 17 A Tehran

Ma'aikatar tattara bayanan sirri ta Iran ta bayyana sunayen maharan da suka kai jerin hare hare ta'addanci a birnin Tehran a Jiya Laraba.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da adadin mutanen da suka rasa rayukansu a jerin hare haren da aka kai a hubbaren Imam Khomeini wanda ya asasa Jamhuriya musulinci ta Iran da kuma na majalisar dokokin kasar ya kai 17 tare da jikkata wasu 46. 

Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar a yau Alhamis ta ce an tantance maharan biyar wandanda Iraniyawa ne, da kuma bayyana kungiyar da suke wa aiki.

Duka dai maharan biyar sannanu ne daga ma'aikatar tsaron kasar wanda suke wa kungiyar wahabiyawa yan takfiriya aiki.

Mutanen dai sun fice daga Iran bayan da kungiyar ta dauke su, inda suka dinga aikata ayyukan ta'addanci a biraren Mosul na Iraki da kuma Raqqa a Syria, bisa jagorancin wani kwamandan na kungiyar Da'esh, mai suna Abu Aisha.

Sun kuma sake dawowa Iran a watan Agusta na shekara data gabata a wani shiri na kaddamar da hare-haren ta'addanci, amman aka wargaza shirin nasu, yayin da wasu daga cikinsu suka tsere.

Ma'aikatar tattara bayannan sirrin ta Iran ta ce ta sakayya sunayen iyalen maharan saboda dalilai na tsaro.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky