Amurka Zata Sanar Da Matsayinsa Kan Yarjejeniyar Nukiliyan Iran

Amurka Zata Sanar Da Matsayinsa Kan Yarjejeniyar Nukiliyan Iran

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa, a yau Talata da misalin karfe 6 na yamma agogin GMT, zai sanar da matsayinsa dangane da yarjejeniyar nukiliyan Iran.

Tashar Almayadeen ta ta bayar da rahoton cewa, wasu majiyoyi na kusa da fadar white house sun ambata cewa, Trump yana fuskantar kakausar suka daga wasu 'yan siyasar kasar, dangane da hankoronsa na ficewa daga wannan yarjejeniya, daga ciki har da wasu daga cikin sanatocin kasar gami da wasu 'yan majalisar wakilai.

A nata bangaren kasar Iran, a ta bakin kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar bahram Qasemi, ta bayyana hankoron Trump na ficewa daga yarjejeniya da cewa ba sabon lamari ba, domin kuwa tun kafin ya dare kan kujerar shugabancin kasar Amurka yake furta haka, kuma bayan shigarssa fadar white house abin da yake nanatawa kenan dare da rana.

Qasemi ya ce Iran tana da matakan da ta za ta dauka kan dukkanin matakin da Trump ya dauka a ficewa ko tsayawa a cikin yarjejeniyar, kuma hakan zai kara fito da fuskar Amurka a fili ko ya ganta kuma ya gane ta.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky