Yawan fararen hula da 'yan ta'addan IS ke garkuwa da su Mosul ya karu

Yawan fararen hula da 'yan ta'addan IS ke garkuwa da su Mosul ya karu

Majalisar dinkin duniya, ta ce yawan fararen hular da 'yan ta'adda IS ke garkuwa da su a birnin Mosul na Iraqi, ya karu zuwa dubu 150 daga dubu 100 da ta sanar a baya

Shugabar sashin bada agajin gaggawa ta Majalisar a yankin, Lise Grande, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AP cewa, 'yan ta'adda na IS suna bude wuta kan duk wani farar hula da yayi yunkurin tserewa daga birnin.

Grande ta ce akalla mutane 7,000 ne aka samu da raunukan harbi a gadon baya, wadanda suka samu, sakamakon yunkrin teserewa daga yankunan da ke karkashin IS da suka yi.

A halin yanzu yawan fararen hular da majalisar dinkin duniya ta yi hasashen zasu tsere daga Mosul ya kai dubu 860, daga dubu 750 da tayi hasashen zasu tsere a baya, sakamakon gwabza yaki da ake tsakanin 'yan ta'adda IS da sojin Iraqi da kokarin murkushe su tun a watan Oktoban bara.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky