Yakin Mosul na kara haifar da matsalar ‘yan gudun hijira a Iraqi

Yakin Mosul na kara haifar da matsalar ‘yan gudun hijira a Iraqi

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yawan fararen hula da ke gujewa yaki a Mosul na Iraqi na neman su gagari kundila, matakin da ya jefa kungiyoyin agaji cikin mawuyacin hali kan hidima da bukatun dubban mutanen.

Hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane dubu dari bakwai yakin Mosul ya raba da gidajensu.

Babbar jami’ar hukumar da ke kula da ayyukan jin kai Lise Grande ta fadi a cikin wata sanarwar cewa yawan fararen hular da ke gujewa gidajensu a yammacin Mosul sun wuce kima.

Mutanen na hijira daga Masul ne cikin mawuyacin hali inda suke shafe makwanni ko watanni ba abinci da ruwan sha mai tabta da magani, a cewar Lise.

Tsawon Watanni bakwai ana gwabza fada a Mosul tun lokacin da dakarun gwamnatin Iraqi suka kaddamar da yaki akan mayakan IS da suka kwace garin a 2014.

Majalisar Dinkin Duniya tace kusan rabin miliyan daga cikin ‘yan gudun hijirar sun fice ne daga watan Fabrairu bayan dakarun Iraqi sun kutsa kai yammacin birnin na Mosul.

Madam Lise ta yi kiran taimako saboda kalubalen kula da bukatun ‘yan gudun gijirar da suke fuskanta sakamakon yawan mutanen da ke ci gaba da tserewa daga yakin na Mosul.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky