Wata Kotun Soji A Kasar Lebanon Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Sheikh Ahmad Asir

Wata Kotun Soji A Kasar Lebanon Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Sheikh Ahmad Asir

Wata kotun soji a kasar Lebanon ta yanke hukuncin kisa kan malamin yan ta'adda Sheikh Ahmad Asir a jiya Alhamis saboda samunsa da laifin kisan sojojin kasar

Tashar Talabijin  ta Presstv a nan Tehran ta ce Major General Hussein Abdullah ne ya jagorancin kotun sojin wacce ta yanke wanda hukuncin a jiya ِakhamis , sannan zata saurari wasu kararrakin na mutane kimani 33 kan irin wannan laifin.

Tsohon mawaki dan kasar ta Lebanon mai suna Fadl Shakeer wanda yake tsananin goyonn bayan Al-asir yana daga cikin wadanda kotun ta yankewa hukuncin zaman kaso na shekaru 15 duk da cewa bai shiga hannu ba. Amma ana zaton yana boye a cikin sansanin yan gudun hijira na Palasdinawa da ke Ain -Al-hilwa mai tazarar kilomita 45 daga birnin Beyrut.

Har'ila yau an gurfanar da dan'uwar Ahmad Asir mai suna Amjad Al-Asir da yayansa biyu Muhammad da Umar  a gaban wannan kotun tare da tuhumarsu da kafa kungiyar yan ta'adda.

An kama Al-Asar ne a cikin watan Augustan shekara ta 2015 a tashar jiragen sama na Rafic Hariri International Airport na Beyrut a lokacinda yake kokarin ficewa daga kasar.

Maigabatar da kasar na gwamnatin kasar ta Lebanon dai ya bukaci kotun ta yanke hukuncin kisa kan wadanda ake tuhuma da ayyukan ta'addanci har 50 sanadiyar kisan sojojin kasar 18 a garin Saida a shekara ta 2013.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky