Trump: A Shirye Nake In Zauna Kan Teburi Tare Da Shugaban Koriya Ta Arewa

Trump: A Shirye Nake In Zauna Kan Teburi Tare Da Shugaban Koriya Ta Arewa

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, a shirye yake ya zauna kan teburin tattauna tare da shugaban kasar Koriya ta arewa Kim Jong-un.

Kamfanin dillancin labaran Reauters ya bayar da rahoton cewa, a daren jiya shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, idan har yanayi ya bada dama, a shire yake ya zauna kan teburi guda tare da shugaban koriya ta arewa domin su tattauna, kuma a cewarsa zai farin ciki da alfahari da hakan idan ta kasance.

Furucin na Donald Trump yana a matsayin sauya kalamansa ne da ke yin barazanar daukar matakin soji a kan Koriya ta arewa, matukar dai ta kara yin gwajin makamanta na ballastic da kuma na nukiliya, sakamakon wannan barazana da Trump ya yi, Koriya ta arewa ta ci gaba da yin gwajin makamanta babu kakkautawa.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky