Takunkumin Karya Tattalin Arziki Ga Koriya Ta Arewa

Takunkumin Karya Tattalin Arziki Ga Koriya Ta Arewa

Zuwa jiya Talata wasu tsauraran takunkumai, wadanda ka iya matsa lamba ga Koriya Ta Arewa ta fannin kudin shiga, sun kama hanyar zama doka, ta yadda ya rage mataki guda kawai.

Majalisar Wakilai ta kada kuri'a kan wani kuduri wanda ke goyon bayan kiraye-kirayen gwamnatin Trump na a dau matakai masu tsauri kan kasar Koriya Ta Arewa.

"Wannan kudurin zai bai wa gwamnati kwarin gwiwa wajen kare Amurka da kawayenmu daga barazanar nukliyar Koriya Ta Arewa ta wajen auna wadanda ke da hannu a daukar matakan takala da gwamnatin Koriya Ta Arewa ta ke yi." a cewar Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Harkokin Kasashen Waje Ed Royce.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky