Syria: Mayakan Kurdawa Sun Kashe 'Yan kungiyar Da'esh Fiye Da 100

Syria: Mayakan Kurdawa Sun Kashe 'Yan kungiyar Da'esh Fiye Da 100

Mayakan na kurdawa sun kashe 'yan ta'addar Da'esh 120 a gundumar Rikkah da ta ke arewacin Syria.

Mayakan na kurdawa sun kashe 'yan ta'addar Da'esh 120  a gundumar Rikkah da ta ke arewacin Syria.

Kamfanin dillancin labarun "Fars" na Iran ya nakalto cewa; A garin al-Dahbakah kadai, mayakan kurdawan Syria sun halaka 'yan Da'esh 52, sai kuma a garin "Sahil al-khsab' da us ka kashe wasu karin 76.

A can garin 'al-safsafah da Ubad' mai nisan kilo mita 4 daga garin al-dhabkah, ana ci gaba da yin fada a tsakanin Kurdawan da kuma 'yan ta'addar Da'esh.

A gefe daya, kwamandan rundunar sojan Rasha ta tsakiya, Sergey Rodskoy, ya ce sun kame wani dan ta'adda da ke dauke da bama-bamai gabanin kai harinsa a kan masu bada taimakon jin kai a yankin Gudha al-sharkiyya.288

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky