Sojojin Siriya Da Dakarun Sa-Kai Sun Kashe 'Yan Ta'adda Fiye Da 100 A Shiyar Yammacin Kasar

Sojojin Siriya Da Dakarun Sa-Kai Sun Kashe 'Yan Ta'adda Fiye Da 100 A Shiyar Yammacin Kasar

Dauki ba dadi tsakanin sojojin gwamnatin Siriya da suke samun tallafin dakarun sa- kai da gungun gamayyar 'yan ta'addan kungiyar An-Nusrah ya lashe rayukan 'yan ta'adda fiye da 100 a yankin da ke arewacin kasar.

Gidan talabijin na Al-Manar na kasar Lebanon ya watsa rahoton cewa: Gungun 'yan ta'addan kungiyar An-Nusrah da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda da suka hada kawance sun dauki matakin kaddamar da harin wuce gona da iri kan sansanin rundunar sojin Siriya da ke yankin arewa maso gabashin garin Hamah a shiyar yammacin kasar Siriya a jiya Juma'a, inda suka fuskanci maida da martani mai gauni daga sojojin Siriya da dakarun sa-kai da suke mara musu baya lamarin da ya janyo halakar 'yan ta'adda fiye da 100 tare da jikkata wasu kimanin 200 na daban.

Gungun 'yan ta'addan sun shirya kaddamar da harin ne a matsayin karya yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a tsakaninsu da sojojin gwamnatin na Siriya a yankunan garin Hamad, amma suka tarar da sojojin gwamnatin Siriya cikin shirin ko-ta kwana lamarin da ya yi sanadiyyar fatattakar ayarin 'yan ta'addan tare da janyo musu mummunar hasarar rayuka.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky