Shugaban Afganistan Ya Ja Kunnen Kasashen Da Suke Goyon Bayan Ayyukan Ta'addancin

Shugaban Afganistan Ya Ja Kunnen  Kasashen Da Suke Goyon Bayan Ayyukan Ta'addancin

Shugaban Afganistan ya gargadi kasashen da suke goyon bayan ayyukan ta'addanci a duniya; yana mai jaddada cewa lokaci yana zuwa da zasu zame saniyar ware, sannan ya yi tofin Alla tsine kan jerin munanan hare-haren ta'addancin da aka kai kasarsa a cikin 'yan kwanakin nan.

A bayanin da ya fitar a jiya Asabar shugaban kasar Afganistan Ashraf Ghani ya yi tofin Allah tsine kan jerin hare-haren ta'addancin da aka kai sassa daban daban na kasar Afganistan a cikin 'yan kwanakin nan, yana mai gargadin dukkanin bangarorin da suke goyon bayan ayyukan ta'addanci a duniya musamman a cikin kasar Afganistan da cewa: Karshensu ya karato domin nan kusa kadan duniya zata dauki matakin kyamatarsu tare da mayar da su saniyar ware.

A cikin 'yan kwanankin nan kasar Afganistan ta yi fama da jerin hare-haren ta'addanci, inda a jiya Asabar wani dan kunan bakin wake ya tarwatsa kansa a cikin wata motar bus makare da jama'a a kusa da makarantar soji ta Marshal Fahim da ke kusa da birnin Kabul fadar mulkin kasar, inda ya kashe mutane akalla 15, kamar yadda a ranar Juma'ar da ta gabata aka kai wasu hare-haren kunan bakin wake a Masallatan Juma'a biyu, daya a birnin Kabul fadar mulkin kasar da kuma lardin Ghor, inda hare-haren suka lashe rayukan mutane fiye da 40 tare da jikkatan wasu adadi masu yawa. Sannan a ranar Alhamis da ta gabata harin kunan bakin wake ya lashe rayukan mutane akalla 43 a lardin Kandahar, haka nan a harin kunan bakin waken da aka kai barikin 'yan sanda da ke birnin Gardez fadar mulkin lardin Paktia a ranar talatar da ta gabata ya lashe rayukan mutane akalla 41 tare da jikkatan wasu masu yawa.

Hakika wannan ba shi ne karon farko da shugaban Afganistan Ashraf Ghani ya gargadi masu goyon bayan ayyukan ta'addanci a cikin kasarsa ba, saboda yau fiye da shekaru uku ke nan yana irin wannan gargadi tare da zargin kasar Pakistan da hannu a shirya makarkashiyar kara kunna wutar rikici da tashe-tashen hankula a Afganistan. Kan haka wani masanin harkokin siyasar kasar Afganistan mai suna Atiqullah Amrkhili ke bayyana cewa: Gwamnatin Pakistan ce ke goyon bayan 'yan ta'addan Afganistan saboda matukar 'yan ta'addan basu samun tallafi daga gwamnatin Pakistan, to babu yadda zasu iya fuskantar sojojin Afganistan.

Manazarta da masharhanta kan harkokin siyasar Afganistan suna ganin baya ga goyon bayan da 'yan ta'addan Afganistan suke samu daga kasashen ketare, sannan kuma akwai sakacin gwamnatin Afganistan na rashin bullo da kwakkwaran shirin tsaro da zai kalubalanci kungiyoyin 'yan ta'adda musamman kungiyar Taliban da na Da'ish da suka yi kaurin suna a kasar, inda gwamnatin Ashraf Ghani ta fi maida hankali kan dambaruwar siyasa tsakaninta da 'yan adawa lamarin da ya bai wa kungiyoyin 'yan ta'adda damar ci gaba da cin karensu babu babbaka a kasar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky