Sayyid Nasrallah: 'Yan Da'esh Ba Su Da Wata Mafita Face Mika Kai

Sayyid Nasrallah: 'Yan Da'esh Ba Su Da Wata Mafita Face Mika Kai

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh da aka fatattaka daga kan iyakokin Siriya da Labanon ba su da wata mafita face kawai su mika kansu ga dakarun gwagwarmaya.

Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi a daren jiya don sanar da nasarar da dakarun kungiyar Hizbullah din tare da sojojin Labanon da Siriya suka samu na fatattakan 'yan kungiyar Da'esh daga kan iyakokin kasashen biyu inda ya ce: Da'esh ba su da wani zabi face su mika kansu, don kuwa an riga da an tarwatsa su wanda hakan ya tilasta musu amincewa da sharadin da muka kafa musu:

Sayyid Nasrallah ya bayyana cewar dakarun Hizbullah da sojojin Siriyan din sun cimma dukkanin manufar da suke son cimmawa yayin yakin da suka kaddamar kan 'yan ta'addan Da'esh din a yankin Qalamoun da kuma cikin kasar Labanon yana mai bayyana nasarar da aka samu na fatattakan 'yan ta'addan  daga kasar Labanon a matsayin "Nasara Ta Biyu" da Labanon ta samu kan makiyanta bayan nasarar farko da ta samu a kan haramtacciyar kasar Isra'ila a shekara ta 2000 lokacin da suka fatattakin sojojin yahudawan daga Kudancin Labanon.

A ranar 19 ga watan Augustan nan ne dai dakarun Hizbullah din tare da sojojin Siriya suka kaddamar da hare-haren fatattakan 'yan Da'esh din daga yankin Qalamoun na kasar Siriya da suka mamaye, a daya bangaren kuma sojojin Labanon su ma suka kaddamar da na su hare-haren kan 'yan Da'esh din da suke rike da wasu yankuna na kasar, lamarin da ya tilasta wa 'yan ta'addan mika wuya bayan kashe wani adadi mai yawa na su da kuma cimma yarjejeniyar ficewa daga yankunan da suka kama din.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky