Sayyid Nasrallah: Trump, "Isra'ila" Da Saudiyya Za Su Ji Kunya Kan Fatan Da Suke Da Shi Kan Rikicin Iran

Sayyid Nasrallah: Trump,

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar shugaban Amurka Donald Trump da kawayensa, na daga haramtacciyar kasar Isra'ila da Saudiyya za su ji kunya dangane da fatan da suke da shi kan rikicin baya-bayan nan da ya faru a Iran, kamar yadda kuma ya sake jaddada cewa matakin da Trump din ya dauka kan Kudus zai zamanto wani mafari da kawo karshen 'Isra'ila'.

Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi a daren jiya Talata da tashar talabijin din Al-Mayadeen ta kasar Labanon inda yace sakamakon rikicin da ke faruwa a Iran zai kunyata shugaban Amurkan da abokanensa da suke ci gaba da kulla makirci wa Iran.

Sayyid Nasrallah ya ce: Trump da wadanda suke tare da shi da suke fatan cewa rikicin zai ci gaba da girma har ya kawo karshen gwamnatin Iran da kuma haifar da fitina a kasar za su sha kunya, don kuwa ko shakka babu al'ummar Iran za su yi maganin wannan fitina, yana mai cewa don kuwa masu zanga-zangar ma 'yan tsiraru ne.

Shugaban kungiyar ta Hizbullah ya ce makiyan al'ummar Iran sun yi amfani da damar da suka samu ne na nuna rashin amincewar da wasu suka yi kan matsalar tattalin arziki da ake fama da shi wajen shigowa da nufin haifar da fitina, yana mai zargin Amurka, Isra'ila da Saudiyya da shigowa cikin lamarin kai tsaye.

Yayin da ya koma kan batun Kudus kuwa, Sayyid Nasrallah ya sake jaddada kalaman da yayi a baya na cewa matsayar da shugaban Amurka ya dauka kan Kudus inda ya ce wannan matsayar za ta zamanto mafarin kawo karshen haramtacciyar kasar Isra'ila.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky