Sayyid Nasrallah: Isra'ila Tana Tsoron Sake Kai Hari Labanon Saboda Karfin Hizbullah

Sayyid Nasrallah: Isra'ila Tana Tsoron Sake Kai Hari Labanon Saboda Karfin Hizbullah

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar zamanin barazanar 'Isra'ila' ya wuce kuma ba zai dawo ba har abada, don kuwa ta san cewa karfin kungiyar Hizbullah ya karu sama da na lokacin yakin shekara ta 2006.

Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a yammacin jiya don tunawa da shekaru 11 da nasarar da kungiyar Hizbullah ta samu a kan haramtacciyar kasar Isra'ila a yakin kwanaki 33 da HKI ta kaddamar a kan kasar Labanon a shekara ta 2006 inda ya ce babban dalilin nasarar da dakarun Hizbullah suka samu a kan 'Isra'ilan' shi ne hakuri, tsayin daka, jaruntaka da kuma dogaro da Allah da dakarun suka yi.

Sayyid Nasrallah ya ja kunnen haramtacciyar kasar Isra'ila da cewa matukar dai wani gigi ya sake dibanta ta kawo wa kasar Labanon din hari, to kuwa za su dibi kashinsu a hannu don kuwa dakarun Hizbullah din a shirye suke su mayar mata da martani mai kaushin gaske.

Yayin da ya koma kan kokarin da shugaban Amurka Donald Trump yake yi na matsin lamba ga kungiyar Hizbullah din don biyan bukatar HKI, Sayyid Nasrallah gwamnatin Amurka ba za ta iya raunana irin azama da karfin da dakarun Hizbullah din suke da shi ta hanyar irin wadannan matsin lambar da take wa kungiyar da sauran kawayenta ba.

A watan Yulin shekara ta 2006 ne dai HKI ta kaddamar da yaki kan kasar Labanon bayan da dakarun Hizbullah din suka kame wasu sojojin sahyoniyawan guda biyu, inda a karshen yakin dai da ya dau kwanaki 33 ana yi, dakarun Hizbullah din suka sami gagarumar nasara a kan sojojin sahyoniyawan da hana su cimma kowane guda daga cikin manufofin da suka sanar wanda daya daga cikinsu shi ne kwato wadannan sojoji guda biyu da dakarun Hizbullah din suka kama.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky