Sarki Salmane Zai Kai Wata Ziyarci A Kasar Rasha

Sarki Salmane Zai  Kai Wata Ziyarci A Kasar Rasha

Sarkin Saudiya Salmane ben Abdelaziz, zai kai wata ziyara a kasar Rasha a tsakiyar watan Yuli mai shirin kamawa, inda zai gana da shugaba Vladimir Poutine a birnin Moscow.

Shafin yada labarai na Press Tv French wanda ya rawaito labarin ya ce, bangarorin biyu zasu tattauna kan batutuwan da suka shafi rikicin kasar Siriya da batun kasar Iraki da yaki da ta’addanci da kuma huldar dake tsakanin kasashen biyu.

Ko baya ga hakan ana tunanin kasashen biyu zasu sanya hannu kan wata yarjejeniyar ta cinikin makamai na Rasha ga kasar ta Saudiya, duk da cewa masana na ganin da wuya Rasha ta sayarwa da Saudiya makaman yaki.

Dama kafin hakan kasashen biyu suna tattaunawa kan yadda zasu fahimci juna akan batutuwan da suke da sabani a kai, kamar rikicin Siriya, yaki a Yemen da kuma sabani na tsakanin Saudiya da Iran.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni