Sannan Ta Bayyana Shirin Kaiwa Sojojin Amurka Hari A Guam

Sannan Ta Bayyana Shirin Kaiwa Sojojin Amurka Hari A Guam

Gwamtanin koriya ta Arewa ta yi watsi da barazanar shugaban Amurka Donal Trump na barin wutan da duniya bata taba gani ba a kanta, ta kuma kara fayyace shirinta ta cilla makaman masu linzami kan sansanin sojojin Amurka mafi girma na Guam a kasar Japan.

Kamfanin dillancin Labaran reuters ya kara da cewa furucin shugaban Trump a ranar Laraba ya fusata gwamnatin kasar Koriya ta Arewa wacce ta kara bayyana shirinta na cillama makaman masu linzami kan sanisanin sojojin Amurka mafi girma a kasar Japan.

Sansanin sojojin Amurka na gGam dai ta na tazarar kilomita 3000 daga kasar Koria ta Arewa a cikin kasar Japan, kuma tana dauke da  sojojin kasar Amurka masu yawa, wanda ya hada da sojojin ruwa da na sama.

General Kim Rak Gyom, babban komandan sojojin Koriya , ya kara da cewa kwararrun yaki da makamai masu linzami zasu kammala seta makaman nasu kan sansanin na Guam a tsakiyar watan Augustan da muke ciki, inda zasu jira umurnin shugaban kasar Kim Jong Un na cillasu.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky