Rasha Ta Halaka 'Yan Ta'adda Fiye Da 2,300 A Syria

Rasha Ta Halaka 'Yan Ta'adda Fiye Da 2,300 A Syria

Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa: Jiragen saman yakinta sun yi luguden bama-bamai a kan sansanonin kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar Syria, inda suka kashe 'yan ta'adda 2,359 tare da jikkata wasu fiye da 700 na daban a cikin kwanaki goma kacal.

Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Rasha Manjor Janar Igor Konashenkov a jiya Asabar ya sanar da cewa: Jiragen saman yakin kasar Rasha sun yi luguden wuta kan sansanonin 'yan kungiyar ta'addanci ta Da'ish da na Jubhatun-Nusrah a sassa daban daban na kasar Syria a cikin kwanaki goman da suka gabata, inda suka yi nasarar halaka 'yan ta'adda 2,359, kuma 16 daga cikinsu manyan kwamandojin kungiyoyin ne, kuma fiye da 400 daga cikin 'yan ta'addan 'yan kasar Rasha ne da sauran kasashen da suke karkashin tsohuwar tarayyar Soviet.

Sanarwar ta kuma fayyace hare-haren sun jikkata gungun 'yan ta'addan da yawansu ya kai 700, kuma jiragen sun kaddamar da hare-haren ne a yankunan da suke garuruwan Adlip da Deir-Zur lamarin da ya zame hasara mafi girma ga kungiyoyin 'yan ta'addan a cikin 'yan watannin baya-bayan nan.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni