Rasha Ta Bukaci A Yi Bincike Kan Kisan Da Amurka Ta Yi Wa Fararen Hula A Mausel

Rasha Ta Bukaci A Yi Bincike Kan Kisan Da Amurka Ta Yi Wa Fararen Hula A Mausel

Gwamnatin kasar Rasha ta bukaci da a gudanar da bincike kan kisan kiyashin da jiragen yakin Amurka suka yi wa fararen hula a garin Mausel na kasar Iraki a cikin wannan mako.

Ministan harkokin wajen kasar Rasha saergey Lavrov, a yau ya bukaci kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya gudanar da zama na musamman domin yin dubi kan hare-haren da Amurka take kaiwa kan fararen hula aMausel da sunan yaki da 'yan ta'adda, musamman ma kisan da ta yi wa fararen hula fiye da 200a  cikin wannan mako.

Lavrov ya ce Amurka da kawayenta suna kai hare-harea  cikin kasashen Syria da Iraki da sunan suna yaki da 'yan ta'addan ISIS, amma kuma a lokaci guda suna kai hari ne kan fararen hula, wanda a cewarsa ya zama wajibi a kan kwamitin tsaro ya dauki mataki kan wannan lamari.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds hanyar Shahidai
Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky