Qatar Ta Gode Wa Iran Akan Kokarinta Na Warware Rikicin Da Ya Fulo Tsakaninta Da Kasashen Larabawa

Qatar Ta Gode Wa Iran Akan Kokarinta Na Warware  Rikicin Da Ya Fulo Tsakaninta Da Kasashen Larabawa

Muhammad bn Abdurrahman Al Thani ministan harkokin wajen Qatar ya jinjinawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma gode mata saboda irin kokarin da take yi wajen magance rikicin da ya kunno kai tsakaninta da wasu kasashen larabawa karkashin jagorancin kasar Saudiyya.

Abdurrahaman Al Thani ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da takwararsa na kasar Rasha Sergei Lavrov inda ya ce kasarsa tana jinjinawa da kuma mika godiyarta ga Iran saboda sanarwar da ta yi na cewa a shirye take ta yi dukkanin abin da za ta iya wajen magance wannan rikicin da ya kunno kai.

Tun dai bayan kunnowar wannan rikicin, Iran ta kirayi kasashen larabawan da su kai hankali nesa kana su yi kokari wajen magance rikicin da ya kunno kai din ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna, tana mai cewa haifar da rikici a yankin nan ba lamari ne da zai amfani kowa ba.

Ita ma kasar Rashan, ta bakin ministan harkokin wajen kasar, Sergei Lavrov ta yi kiran da a kai hankali nesa da kuma yin kokari wajen magance rikicin da ya kunno kai din cikin ruwan sanyi.

A kwanakin baya ne dai kasar Saudiyya tare da kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain da Masar suka sanar da katse alakarsu ta diplomasiyya da kasar Qatar da kuma rufe kan iyakokinsu da kasar saboda abin da suka kira goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'adda da Qatar din take yi da kuma tsoma baki cikin harkokinsu na cikin gida.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky