Pakistan ta kashe Sojojin Afghanistan 50

Pakistan ta kashe Sojojin Afghanistan 50

Rundunar Sojin Pakistan ta ce dakarunta sun kashe akalla sojojin Afghanistan 50 da ke aiki akan iyakar kasar a ci gaba da rikicin kan iyaka da ake yi tsakanin kasashen biyu. Amma Afghanistan ta musanta ikirarin na Pakistan

Rahotanni sun ce an gwabza fadan ne a iyakar Chaman da ta raba Balochistan da ke Pakistan da Kandahar a Afghanistan.

Fararen hula akalla takwas aka kashe, bakwai daga bangaren Pakistan, farar hula guda daga bangaren Afghanistan.

Afghanistan ta zargi Pakistan da takalar fadan.

Manjo Janar nadim Ahmed na sojin Pakistan, ya tabbatar da gwabzawar fadan da ya yi sanadiyar lalata wuraren binciken ababen hawa 5 da kuma raunana mutane sama da 100.

Sai dai kakakin Gwamnan Kandahar, Amim Khpalwak ya ce sojojinsu biyu kawai aka kashe.

Tun Juma’a aka rufe kan iyakar kasashen biyu.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky