Mutane 5 Ne Suka Yi Shahada A Samamen Da Jami'an Tsaron Bahrain Suka Kai Yankin Duraz

Mutane 5 Ne Suka Yi Shahada A Samamen Da Jami'an Tsaron Bahrain Suka Kai Yankin Duraz

Mutanen 5 ne aka tabbatar da shahadarsu a lokacinda jami'an tsaron kasar Bahrai suka kai samame a unguwar Diraz kusa da birnin Manama babban birnin Kasar.

Majiyar tashar television ta al-alam wacce take yada shirye shiryenta da harshen larabci a nan Tehran, ta bayyana cewa matasa 5 wadanda suke gadin gidan Aya. Isa Qasim a yankin Diraz na birnin Manama ne suka yi shahada a jiya Talata bayan wani samamen da jami'an tsaron kasar Bahrai suka kai a gidan malaman.

Har'ila yau ma'aikatar lafiya ta kasar ta Bahrain ta tabbatar da wannan labarin ta kuma kara da cewa ta kawo karshen zaman dirshin da matasa magoya bayan malaman suke yi a gidansa kimani shekara guda da ta gabata. 

Har'ila yau a wani labarin kuma majiyan kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun bayyana cewa jami'an tsaron na Bahrain sun yi amfani da hayakin goba kan mutanen da suke gidan Aya. Isa Qasim. Banda haka sun zuba jami'an tsaro a cikin farin kaya dauke da makamai a yankin don ganin ba wanda ya kawowa malamin taimako.

Labaran baya bayan nan dai sun nuna cewa ana tsare da Aya. Isa Qasim a cikin gidansa da ke yankin na Diraz.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky