Kungiyar Amnesty Ta Zargi H.D. Larabawa Da Aikata Laifukan Yaki A Yemen

Kungiyar Amnesty Ta Zargi H.D. Larabawa Da Aikata Laifukan Yaki A Yemen

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa, Amnesty International, ta zargi Hadaddiyar Daular Larabawa da aikata laifukan yaki a kasar Yemen.

Hadaddiyar Daular Larabawa dai ita ce babbar kawa ga Saudiyya dake jagorantar yaki a Yemen tun cikin watan Maris na shekara 2015 data gabata.

A rahoton data fitar Amnesty, ta zargi Hadaddiyar daular larabawa, da cin zarafi, takurawa, fyade a wasu gidejen yari na kasar ta Yemen.

Rahoton da Amnesty ta fitar a yau Alhamis ya kuma ambato cewa akwai mazaje da dama wadanda batar dasu da karfi tsaiya, bayan cafkesu ba bisa ka'ida ba, wadanda suk wadanan jerin laifuka sun sabawa 'yancin dan adam, kuma tamakar laifukan yaki ne.

Kungiyar ta yi kira ga abokan Hadaddiyar Daular Larabawar dake fakewa da yaki da ta'addanci, musamman Amurka, dasu bayyana sunayen wadanda keda hannu a wannan aika-aikar.

Amnesty International, ta ce kawai ana fakewa da yaki da ta'addanci don cafke 'yan adawa.

A nata bangare dai Hadaddiyar Daular Larabawar ta musanta duk wadanan zarge zargen musamman na cewa tana rike da ikon wasu gidanjen yari a boye a kudancin kasar ta Yemen.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky