kasashen musulmi na ci gaba da nuna goyan bayan Falesdinu

 kasashen musulmi  na ci gaba da nuna goyan bayan Falesdinu

Shugaban kungiyar Hamas Ismail Haniyeh ya kira kasashen musulmai na Duniya da su gudanar da zanga-zanga nuna goyan baya zuwa Falesdinawa dangane da matakin Shugaban Amurka na ayyana birnin Qudus a matsayin babban birnin Isra’ila mako daya da ya gabata.

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana amincewarsa da matsayin Birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila, a wani jawabi da ya sauya manufofin Amurka wanda yanzu haka ya haifar da tashin hankali a Gabas ta Tsakiya.

Shugaba Trump ya ce Isra'ila kasa ce mai ‘yanci saboda haka tana iya sanya babban birnin ta inda ta ke so.

Trump ya ce matakin ba zai sauya matsayin Amurka na samun kasashe biyu tsakanin Isra'ila da Falasdinu ba idan sun amince a tsakanin su.

Tuni wannan batu na Mista Trump ya janyo suka daga shugabannin duniya daban-daban


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky