Kasahen Larabawa Zasu Tattauna A Kan Rikicinsu Da Qatar

Kasahen Larabawa Zasu Tattauna A Kan  Rikicinsu Da Qatar

Ministocin harkokin waje na kasashen Larabawa hudu wadanda suka dorawa kasar Qatar takunkuman tafiye -tatfiye da kuma na diblomasiya zasu hadu a kasar Masar don tattauna batun.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Masar Sameh Shoujry yana fadar haka a jiya Lahadi, ya kuma kara da cewa ministocin harkokin waje na kasashen Masar, Saudia, Bahrain da kuma Hadaddiyar daular Larabawa ne zasu halarci taron, na ranar Laraba 5 ga watan Yuli don tattauan mataki na gaba da zasu dauki idan har kasar Qatar ta kasa ciki wa'adin da suka bata na cika sharuddan da suka shimfida mata kan maida haulda da ita.

Wadan nan kasashe hudu sun katse dangantakar diblomasia da kasar Qatar a cikin watan da ya gabata sun kuma hana tafiye-tafiye tsakanin kasashen su da Qatar, don abinda suka kira tallafawa ayyukan ta'addancin da kasar Qatar take yi.

A kwanakin da suka gabata ne kasashen suka mikawa kasar ta Qatar jiren sharudda guda 13 , wadanda idan ta cikasu zasu kawo karshen takunkuman da suka dora mata. Daga cikin sharuddai dai akwai katse dangantaka da Ira, da kuma Rufe tashar television ta Aljazeera.

Kasar Qatar dai ta musanta zargin da wadannan kasashe suke mata, sannan ta yi watsi da wa'adin kwanaki goma da kuma karin kwanaki biyu da suka bata na cika wadannan sharudda.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky