Indonusiya : Ana Ci Gaba Da Aikin Ceto, Bayan Mummunar Girgizar Kasa

Indonusiya : Ana Ci Gaba Da Aikin Ceto, Bayan Mummunar Girgizar Kasa

Masu aikin ceto a Indonusiya, sun ceto mutane sama da 2,000 yau Litini, bayan mummunar girgizar kasar data yi ajalin mutane a kalla 98 a tsibirin Lombok.

Mafi yawan wadanda girgizar kasar ta yi ajalinsu, 'yan yawan bude ido ne dake a yankin tsaunuka dake arewacin Lombbok.

Girgizar kasar mai karfin maki 6,9 data auku a jiya Lahadi, ta haddasa barnar dubban gidaje da gadoji, mako guda bayan wata girgizar kasar data kashe mutum 17.

Kawo yanzu dai masu aikin ceton na ci gaba da neman wadanda lamarin ya rusa da su, a cikin baraguzan gidaje, masalatai, makarantu da suka ruguje bayan girgizar kasar ta ranar Lahadi.

Hukumomi a arewacin lardin na Lombok, inda nan ne cibiyar girgizar kasar, sun ce girgizar kasar ta lalata kusan kashi 80% na yankin.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky