Harin Saudiyya Ya Hallaka Yara 'Yan Makaranta 39 A Yemen

Harin Saudiyya Ya Hallaka Yara 'Yan Makaranta 39 A Yemen

Wani harin sama da kawancen da Saudiyya ke jagoranta a yakin Yemen, ya yi sanadiin mutuwar yara 'yan makaranta a kalla 39 tare da jikkata wasu mutane 48 na daban a arewacin kasar ta Yemen.

An dai kai harin ne kan wata motar bus dake dauke da yara a lardin Dahyan, dake arewacin Saada, kuma mafi yawancin yaran da lamarin ya rutsa dasu 'yan tsakanin shekara 10 zuwa 14 ne.

Kafin hakan dama kungiyar agaji takasa da kasa ta CICR, dake bada taimako ga asibitin yankin ta ce harin ya yi ajalin mutane 29 galibi yara, wanda a cewarta ya kamata a dinga kare fararen hula a lokutan yaki.

Ita kuwa a nata bangare, wakiliyar asusun kula da yara na MDD, cewa da Unicef, Meritxell Relano, ta ce ta kadu matuka da samun wannan labarin.

Wata sanarwa da kawancen da Saudiyya ke jagoranta kan yakin kasar ta Yemen ya amince da kai harin, tare da kare harin da cewa yana bisa ka'ida, kuma daidai da dokokin kasa da kasa ya ke.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky